Ƙungiyar farar hula mai suna Kaduna Voices United ta sanar da shirinta na gudanar da zanga-zangar gama gari a faɗin Jihar Kaduna. Ƙungiyar na kira da a ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, tare da faɗaɗa binciken da ake yi kan gwamnatinsa bisa zargin take haƙƙin ɗan Adam.
A wata sanarwa da mai kula da ƙungiyar, Nura Basiru, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa za a gudanar da zanga-zangar a manyan wurare daban-daban na jihar, sannan a kammala da babbar taro a babban birnin jihar. Ƙungiyar ta ce manufarta ita ce neman a ɗauki mataki kan abin da ta kira shekaru na danniya, kashe-kashe ba tare da bin doka ba, da kuma rashin mutunta ikon shari’a a lokacin mulkin El-Rufai.
Sun kuma yi nuni da abin da ya faru a Zariya a watan Disambar 2015, inda jami’an tsaro suka yi arangama da mambobin Islamic Movement in Nigeria ƙarƙashin jagorancin Ibraheem El-Zakzaky, lamarin da ya janyo asarar rayukan daruruwan mutane. Ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da za a tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa tare da tabbatar da bin doka da oda.