Arewa Bridge Media GIDA
Politics

MATSALAR TSARO: Wani Lauya Ya Zargi Shugabanni Da Yin Biris Da Kukan 'Yan Arewa, Ya Koka Kan Dakatar Da Malam Alkali Zaria

05 Mar, 2026 2 min karantawa

Wani fitaccen lauya, A.M Jariri, Esq., ya caccaki shugabannin siyasa da na tsaro a Najeriya, gami da shugabannin addini da na al'umma a Arewacin kasar, bisa zargin yin watsi da kisan gillar da ake yi wa al'ummar yankin na tsawon shekaru sama da goma sha shida.

 

Lauyan ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa, inda ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnati da shugabanni suka yi gaggawar daukar mataki kan wani malamin addinin Musulunci, Malam Alkali Zaria, wanda aka dakatar daga gudanar da tafsiri bayan ya soki masu mulki a wani wa'azinsa.

A cewar A.M Jariri, wannan gaggawa da hukumomi da shugabannin Arewa suka yi wajen dakatar da malamin ya saba wa yadda suka yi kunnen uwar shegu da koke-koken al'ummar Arewa da ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga da ta'addanci a kowace rana.


A cikin wani yanki na kalamansa, lauyan ya ce: "Shugaban Kasa, Gwamnoni, Hukomomin Tsaro da dukkanin Malamai da Shugabannin Arewa sun ji caccakar da Malam Alkali Zaria yayi kan masu mulki a wa’azi guda ďaya (Har suka saka aka dakatar da shi daga Tafsir), amma ba su ji koken al’ummar Arewa da kullum ake kashewa sama da shekaru 16 ba."


Ya kara da cewa, wannan yanayi wata bayyananniyar shaida ce da ke nuna cewa shugabannin suna gani kuma suna jin irin halin kuncin da al'umma ke ciki, amma sun zabi su zuba ido. Ya siffanta wannan ko-oho da cewa "tsabar zalunci ne da rainin wayo" wanda yasa aka bar yankin a cikin halin ni-'yasu.


A karshe, lauyan ya kammala sakon nasa da nuna mika al'amarinsa ga mahalicci, inda ya ce, "Allah ya isa!" – wanda ke nuna kololuwar bacin rai da kuma rashin kwarin gwiwa kan shugabannin wajen kawo karshen wannan annoba da ta addabi yankin Arewa.

SAURARI TAKAITATTUN RAHOTANNI

LABARUN DUNIYA

LIVE
TURA ZUWA