Arewa Bridge Media GIDA
Politics

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Daukar Sabbin Sojoji 28,000 Cikin Shekara Guda — COAS

05 Mar, 2026 2 min karantawa

A wani gagarumin mataki na karfafa tsaron kasa da dakile ayyukan ta'addanci, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar sabbin sojoji sama da 28,000 tare da ba su horo a cikin wannan shekarar.

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Gwamnan Jihar Benue, Mista Hyacinth Alia, a gidan gwamnati da ke Makurdi.


Janar Shaibu ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin muhimman matakan da gwamnatin tarayya ke dauka domin farfado da karfin rundunar soji wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi sassa daban-daban na kasar nan.


A cewar Babban Hafsan, baya ga kara yawan jami'an tsaro, rundunar tana kuma fadada dabarunta na yaki da rashin tsaro. Wannan ya hada da yin amfani da karfin bindiga (kinetic) da kuma kulla kyakkyawar hulda da al'umma (non-kinetic) domin samun muhimman bayanan sirri da kuma samun goyon bayan jama'a.


Don nuna aiki da cikawa, Janar Shaibu ya sanar da tura wata sabuwar bataliyar sojoji zuwa karamar hukumar Kwande a jihar Benue, da nufin dakile ayyukan miyagu da kuma tabbatar da tsaro. Ya kuma kara da cewa rundunar za ta kara tura jirage masu saukar ungulu domin gaggawar kai dauki a karkashin aikin Operation Whirl Stroke, wanda ke yaki da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin.


A nasa jawabin, Gwamna Hyacinth Alia ya jinjina wa gwamnatin tarayya da kuma dukkanin jami'an sojin kasa bisa namijin kokarin da suke yi wajen samar da zaman lafiya. Ya bayyana cewa, sakamakon kyakkyawan aikin sojojin, an samu gagarumar nasara inda adadin kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar ya ragu matuka, daga 17 zuwa guda 3 kacal.


A karshe, Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jami'an tsaro cikakken goyon baya don samun dawwamammen zaman lafiya a Jihar Benue da ma Najeriya baki daya.


#TsaronNajeriya #RundunarSoji #ShugabaTinubu #LabaranKasa #ArewaBridgeMedia

SAURARI TAKAITATTUN RAHOTANNI

LABARUN DUNIYA

LIVE
TURA ZUWA