Babbar kotun Najeriya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta shigar kan mataimakin kwamishinan ƴan sanda da aka dakatar Abba Kyari, tare da wanke shi daga zargin ƙin bayyana kadarorin da ya mallaka.
Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa hukumar NDLEA ta kasa gabatar da ƙwararan hujjoji da za su tabbatar da zargin da ake yi wa Kyari a gaban kotu.
A cewar alkalin, shaidun da aka gabatar ba su isa su tabbatar da zargin ba.