"Kamfanin Jiragen Sama na Saudiyya SaudiAirlines zai sake fara zirga-zirga daga Jeddah zuwa Abuja a watan Yuni, ko kuma zuwa watan Janairu na shekarar 2027".
Jakadan Saudiyya a Najeriya Ambasada Yousef Bin Muhammed Al-Balawi, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, a ranar Laraba, a ofishinsa da ke Abuja.
Ya ce dawowar wannan zirga-zirgar jiragen sama za ta ƙara sauƙaƙa tafiye-tafiye tsakanin Najeriya da Saudiyya, tare da ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.