Arewa Bridge Media GIDA
Politics

Babu Wani Tsohon Gwamna da Ya Fi Ƙarfin Doka – Ƙungiyoyin Fararen Hula

26 Feb, 2026 2 min karantawa

Babu Wani Tsohon Gwamna da Ya Fi Ƙarfin Doka – Ƙungiyoyin Fararen Hula

Daga Nura Jamilu Shugaban Masu Rajin Kare Demokradiyya, Kaduna

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula daga sassan Arewacin Najeriya da kuma Kudancin ƙasar nan sun haɗa murya guda wajen jaddada buƙatar fuskantar shari’a ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Ƙungiyoyin sun bayyana cewa, lokaci ya yi da tsarin mulkin Najeriya zai nuna cewa babu wani tsohon shugaba da ya fi ƙarfin doka, komai matsayinsa ko faɗin ikonsa.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, ƙungiyoyin sun bayyana cewa ya zama dole tsohon gwamnan ya fuskanci hukuncin abubuwan da ya aikata a lokacin da yake kan karagar mulki. Waɗannan zarge-zarge sun haɗa da:

Kwashe Kadarorin Al'umma: Yin amfani da ikon mulki wajen ƙwace filaye da gine-gine ba bisa ƙa'ida ba.

Take Haƙƙin Ɗan'adam: Muzanta wa masu adawa da manufofinsa da jami’an tsaro.

Kama Mutane Ba Gaira Ba Dalili: Tsare mutane da masu ra’ayi mabanbanta ba tare da bin hanyoyin shari'a ba.

Shugaban masu rajin kare demokradiyya na Kaduna, Nura Jamilu, ya jaddada cewa ba za su zuba ido ana danne haƙƙin talakawa ba tare da an bayar da lissafi ba. Ya bayyana cewa dukkan tuhume-tuhumen da ake masa yanzu sun zama dole su tafi zuwa ga matakin shari'a domin tabbatar da adalci ga al'ummar da aka zalunta.

A cewar ƙungiyoyin, wannan mataki zai zama darasi ga shugabanni masu ci yanzu cewa mulki na ɗan lokaci ne, kuma akwai ranar sakamako ga duk wanda ya taka doka.

SAURARI TAKAITATTUN RAHOTANNI

LABARUN DUNIYA

LIVE
TURA ZUWA