Arewa Bridge Media GIDA
Politics

YANZU-YANZU: Barayin Daji Sun Dashe Abubuwan Fashewa Hanyar Gusau Zuwa Funtuwa

27 Feb, 2026 1 min karantawa

ZAMFARA, NAJERIYA — Ana sanar da daukacin al'umma cewa yanzu haka babban titin da ya tashi daga Gusau zuwa Tsafe, da kuma hanyar Wanzamai zuwa Funtuwa ba ta biyu, sakamakon wani gagarumin barazana ga rayukan matafiya.

Wannan ya faru ne sakamakon binciken da ya tabbatar da cewa barayin daji sun dasa Abubuwan Fashewa a tsakiyar hanyoyin, tun daga garin Kucheri zuwa Wanzamai, har zuwa hanyar Bilbis dake jihar Zamfara.

A halin yanzu, hotuna da bidiyo da suke fitowa daga wurin sun nuna yadda matafiya da motoci da dama suka makale, inda wasu ma suka kwana a kan hanya cikin fargaba suna jiran ikon Allah da kuma daukin jami'an tsaro.

Ana kira ga daukacin matafiya da su guji bin wadannan hanyoyi a halin yanzu, sannan a yada wannan sanarwa domin ceto rayukan 'yan uwa musulmi da sauran al'umma dake shirin bin hanyar.

Muna fatan Allah Ya bamu mafita na alheri, Ya kiyaye daukacin matafiya.


Majiyar Rahoto: Datti Assalafiy

SAURARI TAKAITATTUN RAHOTANNI

LABARUN DUNIYA

LIVE
TURA ZUWA