Wannan mataki na zuwa ne kwanaki biyu bayan Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Bathiya Wesley, ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party tare da wasu ‘yan majalisa 13.
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Fintiri ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar All Progressives Congress a mazabarsa ta K/Wuro Ngayandi da ke Ƙaramar Hukumar Madagali a ranar Juma’a.
Kafin sauya sheƙar tasa, an ce Fintiri ya yi jerin ganawa da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC domin tattauna batutuwan siyasa da ci gaban jihar.
A ranar Laraba kuma, Mataimakin Shugaban APC na shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya jagoranci wasu manyan shugabannin jam’iyyar zuwa wata ganawa da gwamnan a Gidan Gwamnati da ke Yola. Wani daga cikin mahalarta taron ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa ganawar ta nuna aniyar haɗin kai da tattaunawa domin samar da ci gaba, zaman lafiya da wadata a Jihar Adamawa. Ya ƙara da cewa shugabanci nagari da haɗin gwiwa su ne ginshiƙan gina jihar da za ta kasance mai kwanciyar hankali da ci gaba ga al’ummarta.