Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi (Ɗanmodi), ya karɓo Walida, ‘yar asalin jihar da ake zargin wani jami’in (DSS) ya yi garkuwa da ita.
Lamarin ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Namadi ya yi a ranar Talata, inda ya tabbatar wa da al’umma cewa gwamnati za ta ceto Walida tare da ganin an yi mata cikakken adalci.
Gwamnan, tare da manyan jami’an gwamnatin Jigawa da wakilai daga Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA), sun kai ziyara zuwa babban ofishin DSS, inda aka miƙa musu Walida da misalin ƙarfe 10:44 na daren Laraba.